1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin Ukraine na shiga NATO

Zainab Mohammed Abubakar
June 16, 2023

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Ukraine na dab da shiga gamayyar tsaron kasashen na yammaci.

https://p.dw.com/p/4ShX3
Belgien NATO Verteidigungsminister Treffen Brüssel | Milley, Stoltenberg, Reznikov, und Austin
Hoto: Simon Wohlfahrt/AFP/Getty Images

Ya kuma yi kira da a samar da "tsarin tabbatar da tsaron Ukraine a nan gaba" da zarar yakin da ta ke da Rasha ya kare.

Da yake magana bayan taron ministocin tsaro na kungiyar tsaro ta NATO a Brussels, Stoltenberg ya ce mambobin kungiyar da ke yankin tekun Atlantika sun amince da "aiki don samar da majalisar Ukraine da NATO" inda matsayin Ukraine zai kasance "daidai da na kasashe mambobin kungiyar."

Stoltenberg ya kuma bayyana cewa kungiyar tsaro ta NATO tana daukar matakin Rasha na tura makaman kare dangi zuwa makwabciyarta Belarus da gaske, tare da yin Allah wadai da kalaman da Moscow ke yi masu hatsarin gaske.

Wasu majiyoyi sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa ministocin sun kasa cimma matsaya kan shirin tsaro na farko na kungiyar tun bayan kawo karshen yakin cacar-baka.