Zalensky ya sallami wasu manyan jami'ai
January 24, 2023Talla
Mukaddashin ministan tsaro da mataimakin babban jami'i a fadar shugaban kasar Ukraine sun ajiye aikinsu sakamakon badakalar cin hanci da rashawa.
Ajiye aikin manyan jami'an ya zo ne jim kadan bayan da shugaban kasar ta Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da wasu sauye-sauye a cikin manyan jami'an gwamnatin kan zargin cin hanci da rashawa tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar kasar.