1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta musanta ikirarin Rasha kan fiton hatsi

November 3, 2022

Kasashen Ukraine da Rasha na ci gaba da musayar kalamai kan yarjejeniyar fitar da kayan abinci da ke neman rugujewa. A karshen makon iya ne Rasha ta sanar da janyewa.

https://p.dw.com/p/4J2Zc
Türkei | Ukrainisches Getreide Transport
Hoto: Umit Bektas/REUTERS

Hukumomi a Ukraine, sun musanta ikirarin da Rasha ta yi cewa kasar ta ba da sabbin tabbacin kariya ga jiragen ruwa da ke jigilar hatsi domin farfado da yarjejeniyar nan ta safarar kayan abinci zuwa kasashen duniya.

A jiya Laraba ne dai Rasha ta bayyana cewa ta ba da tabbacin a rubuce, a shirin tattaunawar dawo da batun safarar abincin ta tekun Bahar al Aswad.

A karshen makon jiya ne Rasha ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani cikin watan Yuli, wadda aka sanya wa hannu a Turkiyya.

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa akwai jiragen ruwa masu jigilar kayan abinci guda bakwai da ke kan hanyar fita da hatsin zuwa sassa na duniya.