1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine: Zelenskyy ya roki Isra'ila ta ba shi makamai

March 20, 2022

Shugaban Ukraine ya yi wa 'yan majalisar Isra'ilan jawabi a wannan Lahadi, inda ya bukaci Isra'ilan da ta taimaka masa da makamai musamman ganin yadda ya kuranta sojojinta da cewa sun fi kowa kwarewa a duniya. 

https://p.dw.com/p/48lH8
Wolodymyr Selenskyj
Hoto: Pressebüro des ukrainischen Präsidenten/AP/dpa/picture alliance

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya nemi tallafin makamai daga Isra'ila, yana mai tunasar da Isra'ila yawan Yahudawan da ke zaune a Ukraine.


Shi kan shi Shugaba Zelenskyy dai Bayahude ne, kuma ya nuna bacin ransa ga 'yan majalisar Isra'ila kan yadda Rasha ta kai hari a kushewar tunawa da kisan kiyashin Yahudawan nan na Holocaust da ke a Ukraine. 


Kafin yanzu dai shugaban na Ukraine ya yi irin wannan jawabin ga 'yan majalsiar dokokin Amirka da Jamus da Kanada, inda yake ci gaba da neman a taimaka masa, a zo a yaki dakarun Rasha.


Wannan na zuwa ne a yayin da mahukunta a birnin Kiev suka ce dakarun Ukraine sun yi nasarar halaka manyan kwamandojin yakin Rasha a wannan Lahadi. Sai dai kuma sun zargi Rasha da kokarin kai wa biranen da rikicin bai shafe su ba hari.