Ukraine ta soke taron ƙolin EU na Yalta
May 8, 2012Ƙasar Ukraine ta soke taron ƙoli da aka shirya gudanarwa a birnin Yalta sakamakon sanar da aniyarsu na ƙin halartansa da wasu shugabanni na ƙasashen Turai suka yi. Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar da ke birnin Kiev da ta bayar da wannan sanarwa ba ta ƙayyade ranar da taron na koli zai gudana nan gaba ba.
Shugabannin ƙasashen Turai sama da goma ciki kuwa har da shugaba Joachim Gauk na Jamus ne suka ƙaurace ma taron na Ukraine, sakamakon cin zarafin tsofuwar firaministan ƙasar wato Julia Timochenko da gandurorbobi ssuka yi a gidan yari. Wasu daga cikin shugabannin na Turai ciki har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka ce ba za su halarci bikin buɗe wasannin kwallon kafa na ƙasashen Turai da Ukraine za ta ɗauki baƙwanci ba, matiƙar ba a sako Timochenko ba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar