1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta yunkura don yaki da cin hanci

February 5, 2023

Ministan tsaron Ukraine Oleksii Reznikov ya yi alkawarin gudanar da bincike a ma'aikatarsa bayan wata badakalar cin hanci da ta shafi sojojin kasar, amma ya ki yin murabus daga mukaminsa kamar yadda aka bukata..

https://p.dw.com/p/4N7pN
Ministan tsaron Ukraine Oleksij ResnikowHoto: Genya Savilov/AFP/Getty Images

A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Kiev, Minista tsaro Reznikov ya amince cewar jami'an ma'aikatarsa ta tsaro sun gaza yaki da cin hanci, amma ya yi watsi da yin murabus daga mukaminsa kamar yadda wasu 'yar kasar suka bukata.

 A karshen watan Janairu ne Shugaba Volodymyr Zelensky ya sauke wasu manyan jami'ai daga mukaminsu bayan wata badakalar cin hanci da 'yan jaridu suka bankado, wacce ke da alaka da kwangilar saya wa sojoji abinci. Sai dai a wancan lokaci, ministan tsaro Reznikov ya danganta zargin da marasa tushe.

Wannan dai ita ce badakalar cin hanci da rashawa ta farko da ta barke tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, duk da cewa kasar ta yi kaurin suna a fannin wannan dabi'a.