Ukraine ta zargi Rasha da aikata kisan kiyashi a Bucha
April 4, 2022Rasha dai ta musunta zargin kisan fararen hular tana mai cewa wannan wani sabon salo na kasashen yamma na yin amfanin da kafofin sada zumunta domin bata mata suna. Wannan al'amari dai ya janyon martanin kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya wadanda suka yi kira da a gudanar da bincike dangane da ta'asar tare da shirin kara kakabawa Rasha takunkumi.
A cewar babban mai gabatar da kara ta Ukraine Iryna Venediktova, an gano gawarwakin fararen hula 410 a Bucha kusa da birnin Kiev. Kwanaki kadan bayan sojojin Rashan sun janye daga Bucha da Irpin da Gostomel da Kiev da kuma Tcherneguiv da ke a arewacin kasar domin kara karfafa wa a yankin gabashi da kudanci na Ukraine. Washington,da Paris, da Berlin,da Madrid da London da Majalisar Dinkin Duniya dukkaninsu sun yi tir da Allah wadai da ta'asar da suka kira laifukan yaki da aka yi a garin Boutcha da ke arewa maso yammacin Kiev. Shugaban Kasar Ukraine Volodymr Zelensky ya tabbatar da kisan kare dangin da ya dora alhakinsa a kan sojojin Rasha.
"Yace ina magana akan abubuwan da aka gano a Bucha da sauran garuruwanmu da aka kori 'yan mamaya. An kashe daruruwan mutane, an azabtar da su, an kashe fararen hula jingim a kan tituna. Sojojin Rasha sun aikata kisan kare kiyashi, da fyade da fashi tare da kwasar ganima. Ba za mu taba yarda ba.
Moscow ta musanta kashe fararen hula a yankin na Kiev. Ma'aikatar tsaron Rasha ta yi iƙirarin cewar hotunan gawarwakin da aka yi a kan titunan birnin wani sabon salo ne na gwamnatin kyiev ga kafofin watsa labaran na yamma domin bata mata suna. Rashar ta kuma yi kira da a gudanar da taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin yanke hukunci a kan abin da ta kira tsokanar kiyayya da Ukraine ta yi a Bucha. Sai dai a jawabin da ya yi shugaban Faransa ya ce akwai shaidu ya kara da cewar sun kadu da wannan lamarin wanda ya ce sojojin Rashar suka aikata
Yace akwai shaidu na aikata laifukan yaki da sojojin Rasha suka aikta ya ce muna ba da gundumawar ga Ukraine wajen gudanar da bincike. Haka ma da karin bincike na kasa da kasa. Shariar kasa da kasa za ta yi aiki ga wadanda suka aikta wannan ta'asa za su bayana a gaban kuliya
Kungiyar tarayar Turai ta kira taron gaggawa domin kara kakabawa Rasha sabon takunkumin karya tattalin aziki a kan bukatar Faransa da Jamus ga abinda shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Cholz yake cewa:
"Za mu yanke shawara kan karin matakan da za a dauka tare da kawayenmu a cikin kwanaki masu zuwa. Shugaba Putin da magoya bayansa za su ji sakamakon, kuma za mu ci gaba da baiwa Ukraine makamai domin ta kare kanta daga mamayar Rasha."
A halin da ake ciki kungiyar taryar Turai ta kira wani taro na ministocin harkokin waje da za a yi a ranar 11 ga wannan wata na Afrilu wanda zai shirya babban taron kungiyar da za a mayar da hankali kan batun na Ukaine