SiyasaTurai
Ana boren adawa da mamayar Rasha a Ukraine
March 6, 2022Talla
Jami'an tsaro a birane 21 na kasar Rasha sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da mamayar da Shugaba Vladimir Putin ke yi wa kasar Ukraine.
Hakan na zuwa ne yayin da a Ukraine, Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya zargi dakarun Rasha da yunkurin kai farmaki a birnin Odessa da ke kusa da teku. Zelenskyy ya ce yin hakan mummunan laifi ne a harkar yaki.
Shugabannin Ukraine sun ce a wannan Lahadi, Rasha ta ci gaba da kai hare-hare da jiragen sama a birnin Mykolaiv, inda sojojin Rasha da na Ukraine suka yi musayar wuta.