1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin tallafin kudi na EU wa Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar
May 18, 2022

A wani mataki na taimaka mata saboda yaki da ya daidaita ta, shugabar hukumar gudanarwar tarayyar Turai ta gabatar da shirin karin tallafin wajen Euro biliyan tara ga Ukraine.

https://p.dw.com/p/4BTH9
Brüssel | Ursula von der Leyen | Präsidentin der Europäischen Kommission
Hoto: Olivier Hoslet/dpa/Pool EPA/AP/picture alliance

Von der Leyern ta ce, lokaci yayi da za a fara tunanin yadda za a gina Ukraine, a duk lokacin da aka kawo karshen yaki, inda ta kara da cewar EU na da sha'awar jagorantar aikin sake gina kasar.

A daya hannun kuma, EU za ta kashe makuddan kudi da yawansu zai kai Euro biliyan 300 nan da shekara ta 2030, kafin ta samu 'yancin cin gashin kanta daga dogaro da makamashin Rasha.

A halin da ake ciki dai, wani sojin Rasha da ake zargi da aikata laifukan yaki a Ukraine, a bangaren shari'ar farko da aka kaddamar tun bayan da Rasha ta mamaye kasar, ya amince da duk zarge zargen da aka yi masa. 

Da aka tambayeshi a gaban kotu game da laifuffukan yakin da ke kansa, ciki har da kisan gilla, Sergeant Vadim Shishimarin mai shekaru 21 da haihuwa, ya amsa aikata laifukan.