Unesco: Jahilci na kara kamari a duniya
September 6, 2018Talla
Hukumar ta ce daga cikin mutanen da ke zaune a cikin wannan yanayi na jahilci miliyar 102 matasa ne 'yan tsakanin shekaru 15 zuwa 24 da ba su iya karatu da rubuta ba. Hukumar ta Unesco ta ce lallai adadin mutanen ya ragu idan aka kwatanta da alkalumman shekarar da ta gabata, sai dai ta ce sabanin bai taka kara ya karya ba.
Rahoton ya kuma bayyana cewa kasar Jamus na fama da matsalar mutanen da suke rayuwa da wannan jahilci inda yanzu haka kashi 12 daga cikin dari na matasa a kasar ba su iya karatu da rubutu kamar yadda ake bukata ba.