1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNESCO: 'Yan jaridar da aka kashe sun karu

January 16, 2023

Alkalumman Hukumar Kula da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO na nuni da cewa, adadin 'yan jarida da aka kashe a bara sun karu da kaso 36 cikin 100.

https://p.dw.com/p/4MHDU
Babbar daractar UNESCO Audrey Azoulay
Hoto: Lafargue Raphael/ABACA/picture alliance

Alkalumman dai sun nuna cewa 'yan jaridar da aka kashe a duniya, sun karu zuwa 86 daga 55 a shekarar 2021. UNESCO ta ce rabin adadin wadanda aka kashe a yankunan Latin Amirka da kuma Caribbean suke, kana yawancin 'yan jaridar an halaka su ne a kasashen Mexico da Ukarine da kuma Haiti.

Babbar Daraktar hukumar Audrey Azoulay ta ce, ya zama wajibi hukumomi su kara matsa kaimi wajen kawo karshen wadannan laifuka tare da hukunta wadanda ke da hannu a ciki. Ta kara da cewa, a baya dai, adadin 'yan jaridar da ake kashewa ya ragu daga shekarar 2018 zuwa 2021. Kusan dai 'yan jaridar na gamuwa da ajalinsu ne a bakin aikinsu ko kuma yayin da suke hanyarsu ta komawa gida, lamarin da UNESCO ta ce na nufin 'yan jarida ba su da wata mafaka.