UNCHR ta ja hankali kan 'yan gudun hijirar Siriya
July 5, 2018Talla
Babban jami'in majalisar Grandi, ya ce akwai wadanda ke cikin tsaka mai wuya da ke bukatar taimakon gaggawa a sanadiyar raunin da suka ji, ya ce kamata ya yi masu fada da juna su tsagaita bude wuta don bai wa jami'ai damar kwashe su don yi musu magani.
Ya kuma yi kira na neman taimakon kasar Jordan, kan ta bude kofofinta don bai wa wadanda rikicin Siriyan ya shafa shiga kasar, Mista Grandi ya ce sauran kasashen duniya, su tallafawa kasar ta Jordan da kudi don daukar dawainiyar 'yan gudun hijirar.