Annobar corona za ta hana yara karatu
September 3, 2020Talla
Babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi, ya ce bayan yanayi na mawuyacin halin da suka fuskanta a baya, bai dace a hanasu samun ingantacciyar makoma ba a yanzu saboda haka ya bukaci a dage don basu ilimi.
Hukumar kula da 'yan gudun hijirar dai na fargabar makomar yaran ne duk da abinda zai biyo bayan karshen annobar Corona, inda ta ke hasashen mafi yawancinsu za su dakatar da zuwa makaranta bisa fuskantar wasu tarin matsaloli na rayuwa ciki harda na daukar dawainiyar karatunsu da na iyali.