UNICEF: An wulakanta yara a duniya
December 28, 2018Talla
Asusun kula da yaran na kasashen duniya UNICEF, ya ce daga watan Janairu zuwa yanzu, bangarori masu rikici a duniya sun yi ta yi wa rayuwar yara galatsi mai munin gaske.
Asusun ya lasafto kasashe irin su Siriya da Yemen da Kwango da Najeriya da Sudan ta Kudu, a matsayin kasashen da matsalar ta fi kamari a cikinsu.
A kasar Myanmar an yi wa yara da dama fyade da auren dole, a cewar UNICEF, yayin da a Afghanistan yara kimanin dubu biyar aka kashe, sai kuma a Somaliya da aka tilasta wa 1,800 shiga aikin soja.
Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce tilas ne a sama wa matsalar magani cikin gaggawa.