UNICEF: Rikicin Gabas ta Tsakiya na hallaka yara
February 5, 2018Talla
Asusun kula kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce watan Janairun 2018, ya kasance bakar wata ga kananan yara ganin yadda aka zubda jinin yara a kasasahen Iraki da Siriya da Falatsinu da Yemen da kuma Libiya.
UNICEF ta ce ba za a bari jinin yaran ya bi ruwa ba, wajibi a su taimaka a daga muroyoyin wadanda ba hali su bayyana kukansu. A don haka suke kira da a kawo karshen afkawa kananan yara a lokutan yaki.
Wasu alkaluma da MDD ta wallafa ya nuna cewa an kashe kananan yara 59 a Siriya, yayin da kasar Yemen ke biyemata cikin kashen da akafi salwantar da rayuwar yara.