1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF ta yi tir da karuwar tozarta wa kananan yara a Sahel

May 30, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da karuwar tilasta wa yara shiga ayyukan da suka fi karfinsu a wasu kasashen yankin Sahel da ke fama da ayyukan ta'addanci tsawon shekaru.

https://p.dw.com/p/4gROG
Hoto: Getty Images/AFP/S. Glinski

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya bayyana takaicin karuwar da aka gani na 70% kan abin da ya shafi tozarta wa yara a kasashen Mali da Burkina da ma Jamhuriyar Nijar.

Dukkanin kasashen da aka bayyana dai kasashe ne da ke fama da matsalolin 'yan bindiga masu da'awar jihadi da ma wasu nau'uka na rashin zaman lafiya.

Haka ma bakin dayan kasashen uku, na karkashin gwmanatoci ne da sojoji ke mulki, bayan kwace iko cikin shekara ta 2020.

UNICEF din ya ce musamman cikin watannin karshe ne shekarar da ta gabata ne aka soma fahimatar kazantar matsalar tozartar da rayuwar kananan yaran a wadannan kasashe.

Daga cikin abin da ake yi musu kuwa, har da sanya su cikin kungiyoyin ta'addanci a matsayin mayaka.