UNICEF ya ce an sami sauki a auren wuri a duniya
March 6, 2018Wani rahoton da asusun na UNICEF ya fitar ya ce kokarin da duniya ta yi na wayar da kan jama’a ya taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalar auren na wuri ga ‘yan mata kanana da suka kai miliyan 25 a kasashen da ke kudancin nahiyar Asiya, daga shekarar 2008. Sai dai asusun na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce in ba an tashi ba, akwai ‘yan mata miliyan 150 da ke kan hadarin shiga wannan tarkon na aure suna kasa da shekaru 18 da haihuwa nan da shekara ta 2030, shekarar da kuwa ake burin ganin an cimma yaki da wannan dabi’a.
Babban dai abin da sabbin alkaluman suka nunar, shi ne a yanzu kashi 15 cikin dari ne saukin da aka samu, daya kenan cikin ‚‘yan mata biyar da ake yi wa yuren na wuri, a shekaru goma da suka gabata. A kasashen kudancin nahiyar Asiya, abin da ya fito fili shi ne ilimantar da kananan ‘yan mata da nasarar fadakar da jama’a da gwamnatoci suka yi, su ne suka taimaka wajen rage miliyoyin wadanda ke shiga tarkon.
Akalla dai akwai mata miliyan 650 da aka aurar da su tun suna kanana. 'Yan mata miliyan 12 ne ake yi wa hakan a kowace shekara. A kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara alkaluma sun yi nunin cewa a kasar Habasha ne wato Ethiopia aka sami sauki daga cikin kasashe biyar da suka yi kaurin suna a wannan lamari.