Nijar: Fargabar UNICEF kan tallafa wa yara
August 21, 2023A cikin sanarwar da ya fidda a wannan Litinin Asusun ya yi shelar cewa kafin juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 27 ga watan Yuli dama yara 'yan kasa da shekaru biyar miliyan guda da rabi a Nijar na fama da cutar tamowa sannan kuma wasu dubu 430 na fama da matsanancin nau'i na cutar.
UNICEF ya kuma kara da cewa katse wutar lantarki da Najeriya ta yi biyo bayan matakin matsa lamba ga sojojin da suka kifar da gwamnati da ECOWAS ta dauka ya kara dagula al'amura tare kuma da haifar da barazanar lalacewar alluran da aka tanadar a asibitotcin kasar domin kula da yara.
Karin bayani: Tamowa na barazana ga rayuwar kananan yara
Asusun ya yi kira ga masu ruwa da tsakki a kan dambarwar juyin mulkin Nijar da su gaggauta buda wa ma'aikatansa kofofin shiga Nijar domin isar da kayan agaji da suka makale a kan iyakokin kasar tare kuma da kiran masu hannu da shuni da kadda su katse tallafin da suke ba wa Nijar a fannin kula da yara.