1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF: Za a haifi yara dubu 395 a ranar farko ta 2019

January 1, 2019

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce yara dubu 395 ne ya yi hasashen za a haifa a wannan rana ta sabuwar shekarar 2019 a duniya.

https://p.dw.com/p/3AqKJ
Südsudan Neugeborenes in Juba
Hoto: Getty Images/AFP/S. Glinksi

Kashi daya cikin kashi hudu na yaran da za a haifa a cewar UNICEF, za a haife su a kudancin Asiya, inda a Indiya kadai za a haifi yara dubu 70 a yau. A kasar China acewar asusun, yara dubu 45 ne za a haifa. 

Sai kuma nahiyar Afirka da Najeriya ke kan gaba da yawan yaran da za a haifa, za su kai dubu 26.

Amma fa UNICEF na matukar nuna rashin jindadi, saboda galibin yaran ba za su sami kulawar da ta dace da su ba.

Don hakan ne ma take kiran gwamnatocin duniya su mike tsaye wajen ganin an bai wa iyaye mata tare da jariransu kulawar gaske.