1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVenezuela

Venezuela janye gayyatar jami'an EU a zabenta

May 29, 2024

Gwamnatin Venezuela, ta soke gayyatar jami'an sa ido na kungiyar Tarayyar Turai wadanda za su sa ido a kan zaben shugaban kasar da za a yi cikin watan Yuli da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4gQxd
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela
Shugaba Nicolas Maduro na VenezuelaHoto: Zurimar Campos/AFP

Gwamnatin ta Venezuela ta kafa hujja da abin da ta kira takunkuman mulkin mallaka da Tarayyar ta kakaba wa kasar a matsayin hujjar janye gayyatar da ta yi wa jami'an.

Tarayyar Turan daga nata bangaren, wacce ta kakaba wa Venezuela takunkumai a shekarar 2017, ta yi kira ga kasar da ta sake nazarin wannan mataki da ta dauka.

Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela dai na neman zabe karo na uku, ya yin da tsohon jami'in diflomasiyya Edmundo Gonzalez ke wakiltar gamayyar jam'iyyun hamayya.

Shugaba Maduro tun da fari, ya amince da karbar baki masu sa ido daga ketare, yayin kuma da a gefe guda yake tsananta wa 'yan hamayya a kasar.