1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela: Jam'iyyar Shugaba Maduro ta yi rinjaye a majalisa

Abdul-raheem Hassan
December 7, 2020

Shugaba Nicolas Maduro na kasar Venezuela ya samu gagarumar rinjaye a majalisar dokokin bayan gudanar da zabe mai cike da tsarkakiya a karshen mako.

https://p.dw.com/p/3mKYN
Venezuela Parlamentswahlen Wahlkampf Maduro
Hoto: Ariana Cubillos/AP Photo/picture alliance

Ana ganin kauracewa zaben da 'yan adawa suka yi ne ya ba wa jam'iyyar Maduro ta PSUV samun nasara a zaben majalisar dokokin, inda jam'iyyar United Socialist Party of Venezuela ta samu nasara da kashi 68 cikin 100, yayin da sauran jam'iyyu suka samu kashi 18 duk da kiran kauracewa zaben.

Masu sa ido kan zabe na kasa da kasa kamar EU da OAS ta Amirka, sun ki tura wakilai saboda ikirarin rashin tsara gudanar da zaben kan tafarkin dimukuradiyya. Madugun adawa Juan Guiado ya ce zaben cike yake da magudi.