1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Viktor Yanukovich ya ce har yanzu shi ne shugaban Yukren

February 28, 2014

Hambararen Shugaban Yukren ya yi bayyanar farko a gaban mutane tun bayan tunbuke shi daga madafun iko

https://p.dw.com/p/1BHkh
Hoto: Reuters

Viktor Yanukovich wanda yanzu haka ya ke kasar Rasha, ya zargin cewa ya fuskanci barazana kan rayuwarsa daga masu ra'ayin rikau, abun da ya tilasta masa ficewa daga kasarsa.

Ya dage cewa babu gudun da ya yi daga kasar, kuma yana shirye ya tabbatar da kare makomar kasar, sannan ya ce har yanzu shi ne halartaccen shugaba.

Wannan lokacin da shugaban gwamnatin wucin gadi na Yukren Olexander Turchynov ya saka hannu kan ayar dokar fatattakar babban hafsan sojin kasar Admiral Yuriy Ilyin, wanda aka nada shi kan mukamin dai dai lokacin da ake tsakiyar boren neman kawar da shugaba Yanukovich daga kan madafun iko.

Ministan harkokin cikin gida na kasar ta Yukren ya zargi dakarun kasar Rasha da mamaye filaye biyu na saukan jiragen sama, masu mahimmanci cikin yankin Crimea mai kwarya-kwaryar cin gashin kai.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kira kan kare Yukren daga fadawa cikin mawuyacin hali, kamar yadda fadar mulkin kasar ta ce.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman