1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya yabawa dakarunsa a Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 3, 2022

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya nunar da cewa dakarun kasarsa na yin aiki yadda ya kamata a hare-haren da suke kai wa makwabciyar kasa Ukraine.

https://p.dw.com/p/47yQN
Vladimir Putin
Shugaba Vladimir Putin na RashaHoto: Mikhail Klimentyev/Kremlin/Sputnik/REUTERS

Vladimir Putin ya bayyana cewa dakarun kasar tasa na yin aiki kamar yadda aka tsara, tare da yaba musu da kuma ayyana su a matsayin gwaraza. A wata hira da ya yi da gidan talabijin Putin ya yi ta kawo zarge-zarge da ya gaza kawo kwakkwarar shaida a kan sojojin Ukraine, inda ya ce suna tsare baki 'yan kasashen ketare tare da yin amfani da su a matsayin garkuwa daga hare-hare.

Jawabin na Putin dai na zuwa ne, jim kadan bayan da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya nunar da cewa, yana bukatar tattaunawa da shugaban kasar ta Rasha domin shawo kan matsalar. Zelenskyy ya ce tilas ne ya tattauna da Putin domin kuwa a yanzu shi kadai ne ya kamata ya tunkare shi. A hannu guda kuma, shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bukaci mahukuntan na Moscow da su bayar da damar kai kayan jin kai ga mutanen da yaki ya rutsa da su a Ukraine din. Von der Leyen ta wallafa wannan bukata ne a shafinta na Twitter, tana mai cewa mutanen na cikin tsananin bukatar taimako.