Vladmir Poutine ya kai ziyara farko a Iran
October 16, 2007Shugaban ƙasar Russia Vladmir Poutine,, ya sauka a ƙasar Iran, inda zai halarci taron shugabanin ƙasashen da ke kewaye da kogin Caspienne.
Wannan itace ziyara farko da wani shugaban Russia ya taɓa kaiwa a ƙasar Iran tun shekaru fiye da 60 da su ka wuce.
Kwanaki 2 kamin fara wannan ziyara Jami´an leƙen asirin Russia, sun ce sun bankaɗo wata maƙarƙashiyar harin ta´adanci da aka kitsawa Poutine a lokacin wannan ziyara, saidai duk da haka,
Shugaban na Russia ya yanke shawara gudanar da wannan ziyara.
A nasu ɓangare hukumomin Teheran, sun ƙaryata wannan rahoto.
Poutine tare da sauran shugabanin ƙasashe 4, na kewayen kogin Caspienne, za su halarci wani taron a ƙasar ta Iran, domin masanyar ra´ayoyi, a game da mu´amiloli daban-daban da ke tsakanin su.
Vladmir Poutine da takwaran sa na Iran, Mahamud Ahmadinedjad, za su anfani da wannan dama, domin tantana batun rikicin makaman nuklea.