1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Vladmir Poutine, yayi kiran Iran ta bada ansa tambayar turai da Amurika a game makaman nuklea.

July 4, 2006
https://p.dw.com/p/Buri

Shugaba Vladimir Putine na Rasha yayi kira ga hukumomin Iran, da su gaggauta bada ansa ga tayin da ƙasashen turai da Amurika su kayi masu, a game da watsi da aniyar ƙera makaman nuklea.

Poutinen yayi wannan kira yau, a yayin da ya ke jawabi a taron ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu kare haƙƙoƙin jama´a, da ke wakana a birnin Mosko.

Poutine da ke ɗaya daga shugabanin ƙasashen da ke nuna goyan baya ga Iran, ya ce wajibi ne, HukumominTeheran, su bayyana matsayin su, kamin taron shugabanin ƙasashen G8, da zai wakana ranar 15 ga watan da mu ke ciki a ƙasar Rasha.

Idan dai ba a manta ba, ranar 6 ga watan da ya gabata,ƙasashen turai da Amurika, su ka gabatar da tayin Iran ta yi wasti da aniyar ta, ta ƙera makaman nuklea, to amma ba da wata wata ba, Ali Larjani, shugaban tawagar Iran a tantanawar da ake ke kan wannan batu, ya ce babu gudu babu ja da baya.

Gobe laraba idan Allah ya kai mu, Larijani,za shi sadu da sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai Havier Solana, domin ci gaba da masanyar ra´ayoyi.