Volkswagen zai kori dubban ma'aikata
October 28, 2024 Daniela Cavallo Jagoran majalisar gudanar da kamanin Volkswagen shi ne ya fada wa ma'aikatan kamfanin hakan a wannan Litinin, yayin wani taro da aka yi tsakanin jami'an kamfanin da ma'aikatansa. Shugaban yace daukacin sassan kamfanin kera motocin koda ba a rufe su ba amma dole za a rage ma'aikata daga daraktoci izuwa kasa. Shugaban majalisar gudnawar ya kuma ce yanzu suna jiran abin da hukumar zatarwa za ta fito ta fada a hukumance, sai dai kuma ya gargadesu da kada su kawo rudani a kasar Jamus, domin katafaren kamfanin Volkswagen wato VW a taikaice, yana daya daga cikin abin da ke samarwa kasar Jamus kudin shiga. Tuni dai suma kungiyoyin kwadago suka sha alwashin sai inda karfinsu ya kare, amma ba za su taba barin kamfanin ya dau wannan matakin da zai jawo dubban mutane su rasa aiki a kasar ba. Kamfanin VW yana da cibiyoyin kera mota 10 a fadin kasar, kuma yanzu hatta gwamnatin Tarayyar Jamus ta damu da matakin, inda tunin shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ce bai kamata kuskuren da masu gudanar da kamfanin suka yi ya shafi dubban kananan ma'aikata ba. Kamfanin dai yana fama da matukar talauci, inda yanzu ya ke fiskantar kalubale daga kasar China musamman wajen kera motocin dake amfani da lantarki. Kuma rugujewar arzikin kamfanin ya samo asali ne tun faruwar annobar corona.