1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zelensky na son tattaunawa ta hakika

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
March 19, 2022

A yayin da aka shiga mako na hudu na gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine, Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce tattaunawar zaman lafiya ta hakika ce kadai ka iya ba wa Rasha damar tsira daga kangi.

https://p.dw.com/p/48iej
Ukraine Kiew | Mehrere Gebäude nach Angriffen zerstört
Hoto: Andre Alves/AA/picture alliance

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Mosko za ta amince da hawa kan teburin tattaunawa ta hakika da zummar samar da zaman lafiya don kaucewa kasar fadawa cikin wani mawuyacin kangin da zai dauki dogon lokaci.

Mr. Zelensky da ke jawabi a wani sashin gidaje da ke kufai a daren ranar  Juma'a, ya ce tattaunawa ce kadai ka iya ba da damar tsira daga mummunan ta'adin da Rasha ta aikata a Ukraine. "Lokaci ya yi na maganar tsagaita buda wuta, lokaci ya yi na dawo wa Ukraine bangarorinta da aka mamaya, lokaci ya yi da ya dace a yi wa Ukraine adalci."

Kalamun shugaban na zuwa ne a yayin da yakin da ake gwabza wa tsakanin Ukraine da Rasha ya shiga mako na hudu. Rundunar tsaron Rasha ta shiga har cikin birnin Marioupol da ke kudanci.

Duk wannan na zuwa a yayin da har yanzu aka kasa cimmam matsaya a tattaunawar da aka soma kan batun tsagaita wuta tsakanin tawagogin kasashen byiu, to amma Rasha ta ce da akwai yiwuwar Ukraine ta yi na'am da shawarar da ta bata a baya na kasancewa kasa a tsaka-tsaka kwatankwacin Ostiriya da Sweden, kalamun da kakakin tawagar Ukraine a tattaunawar ya ce ba haka take ba.