Kamfanin motocin Volkswagen zai biya diyya
May 26, 2020Talla
Hukuncin ya bada dama ga wadanda suka gabatar da kara su mayar da motocin da suka saya wadanda aka yi kwange na tauye hayakin da suke fitarwa.
Wadanda suka mayar da motocin za a biya su wani kaso na kudin da suka saya, sai dai kotun ta ce yawan kudin da za a mayar zai dogara ne da nisan tafiyar kilomitan da kowace mota ta ci tun bayan sayar da ita.
Hukuncin na daga tabargaza ta baya bayan nan da kamfanin motocin na Volkswagen ya tafka wanda aka bankado a shekarar 2015 yayin da aka gano ya yi kwangen tauye hayakin da motar ke fitarwa.
Hukuncin dai na iya yin tasiri akan wasu dubban kararraki da ke gaban shari'a wadanda ba a kammala su ba.