1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa zai gaji al-Baghdadi a IS

Gazali Abdou Tasawa
October 28, 2019

Kwana daya bayan kashe jagoran kungiyar IS Abu bakr al-Baghdadi, masana sun soma yin hasashe kan mutuman da zai gaje shi a shugabancin kungiyar.

https://p.dw.com/p/3S6kA
Abu Bakr al-Bagdadi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/

Kwana daya bayan kashe jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi a wani harin da sojojin Amirka suka kaddamar a mabuyarsa da ke a Siriya, da ma kuma kakakinsa Abu Hassan Al-Muhajir, yanzu haka hankalin duniya ya karkata ga neman sanin mutuman da kungiyar ta IS za ta nada a matsayin sabon shugabanta. Kawo yanzu dai shafukan farfaganda na kungiyar ta IS ba su tabbatar ko kuma karyata labarin mutuwar jagoran kungiyar ba, balantana batun maye gurbinsa.

Sai dai wasu masana na ganin akwai yiwuwar kungiyar ta nada Abou Othman Al-Tounis dan asalin kasar Tunusiya da ke zaman shugaban majalisar mashawarta ta kungiyar ko kuma Abu Saleh al-Jouzrawi da aka fi sani da sunan Hajj Abdallah dan asalin kasar Saudiyya wanda shi ne shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar ta IS.

 Sai dai masanan na ganin akwai yiwuwar a samu tawaye a cikin kungiyar ta IS idan aka nada daya daga cikin wadannan mutane biyu kasancewa ba daya daga cikinsu da ya fito daga Siriya ko iraki kasar Al-Baghdadi kasashen da mafiyawancin mayakan na IS suka fito.