1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa zai maye gurbin Juncker?

Yusuf Bala Nayaya
May 28, 2019

Majalaisar Tarayyar Turai ita ke da hurumi na amincewa da sabon shugaba, abin da zai kai ga zama tsakaninsu da shugabanni na EU.

https://p.dw.com/p/3JKOJ
Belgien Brüssel Hauptquartier der EU Kommission
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/M. Spatari

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Tajani ya ce 'yan majalisar sun yi amanna sabon shugaban Hukumar Tarayyar Turai za a zabo shi ne cikin 'yan takara da ke kan gaba daga rukuni-rukuni na 'yan siyasar da ke a majalisar.

Wannan dai zai bude sabon babi na tankiya da wasu shugabanni na Kungiyar EU wadanda ke da burin ganin an fadada hanyoyi da za su kai ga zabin wanda zai gaji Jean-Claude Juncker.

Majalaisar Tarayyar Turai ita ke da hurumi na amincewa da sabon shugaba, abin da zai kai ga zama tsakaninsu da shugabanni na EU. Har ila yau cikin watanni da ke tafe za a zabi shugabanni da suka hadar da na majalisar gudanarwa da majalisar ta EU da na Babban Bankin Turai da shugabancin harkokin kasashen waje na kungiyar. Zabukan da ke da alaka kuma ake tafka muhawara a kansu.