Wadanda suka fi cin kwallo a gasar zakarun Turai
'Yan wasan uku da ke gaba wajen cin kwalo a wasan cin kofin zakarun Turai Cristiano Ronaldo, Lionel Messi da Karim Benzema, yanzu sun fice daga wasannin nahiyar 'yan wasa biyu Thomas Müller da Robert Lewandowski.
Zlatan Ibrahimovic - kwallaye 48
Dan wasan gaba na Sweden, domin haka babu mamaki yadda Zlatan Ibrahimovic ya jefa kwallaye 48 a gasar wasannin cin kofin zakarun Tutai lokacin da ya yi wasa a kungiyoyi shida: Ajax Amsterdam (6), Juventus Turin (3), Inter Milan (6), FC Barcelona (4), AC Milan (9) da Paris St. Germain (20). Amma bai taba lashe kofin zakarun Turai ba.
Andriy Shevchenko - Kwallaye 48
Dan kasar Ukraine kamar Ibrahimovic, Andriy Shevchenko shi ma ya jefa kwallaye 48 a wasannin cin kofin zakarun Turai. Amma ba kamar dan Sweden ba, shi Shevchenko ya taba lashe gasar a shekara ta 2003 tare da kungiyar AC Milan ta Italiya. Dan wasan gaba ya jefa kallaye 29 lokacin da yake AC Milan, 15 yana kungiyar Dynamo Kiev sanna kuma hudu tare da kungiyar Chelsea ta Ingila.
Alfredo di Stefano - Kwallaye 49
Dan wasan gaban kasar Ajentina da da ya shafe shekaru 11 da kungiyar Real Madrid. A lokacin ana kiran kofin zakarun nahaiyar Turai da sunan kofin Turai. shi dai Alfredo di Stefano ya taka muhimmiyar rawa musamman daha shekarar 1956 zuwa 1960 inda ya jefa kwallaye 49. Dan Ajentinan ya rasu a shekara ta 2014, marigayin ya kasance daya daga cikin fitattun 'yan wasa na duniya.
Thierry Henry - Kwallaye 50
Dan wasan gaba na Faransa ya jefa kwallaye rabin 100 a tsawon lokacin da ya yi wasanni a gasar ta neman cin kofin zakarun Turai: S Monaco (7), Arsenal FC (35) da FC Barcelona (8). A shekarar 1998 ya lashe kofi tare da tawogar kunguyar Barça. Akwia kuma mutum-mutumin Henry na tagulla a filin wasan Arsenal. Dan wasan na Faransa yana cikin kudin litattafin tarihi na duniya na Gunners.
Thomas Müller - Kwallaye 54*
Gasar cin kofin zakarun Turai da Thomas Müller, sun dace da juna. A shigar sa na farko, kungiyar Bayern Munich ta doke Lisbon 7 da 1, a watan Maris na shekarata 2009, lokacin dan shekara 19 da haihuwa ya jefa kwallonsa farko daga cikin 53 da za su biyo baya zuwa yanzu. Ya lashe gasar sau biyu a shekara ta 2013 da 2020 tare da kungiyar Bayern Munich. (Wannan zuwa daya ga watan Oktoba na 2024).
Ruud van Nistelrooy - Kwallaye 56
Dan wasan gaba na Netherlands, Rutgerus Johannes Martinus van Nistelrooij ya jefa kwallaye lokacin da ya yi wasa tare da kuniyoyi uku a wasannin cin kofin zakarun Turai: PSV Eindhoven (kwallaye 8), sai Manchester United (kwallaye 35) sannan kuma Real Madrid (kwallaye 13). Van Nistelrooy bai taba lashe kofin zakarun Turai ba, amma sau uku yana zama wanda ya fi cin kwallaye.
Raúl Gonzalez Blanco - Kwalalye 71
Raúl ya zama shahararren dan wasan Real Madrid. Ya dade a matsayin jagoran 'yan wasa kusan fiye da kowane dan wasa. Wasanni 550 ya yi tare da tawogar kungiyar ta Sifaniya, kuma 132 daga ciki na wasannin kofin kofin zakarun Turai. Sau uku yana lashe kofin tare da Real. Shi dai Raúl ya jefa kwallaye 71 a wasannin na cin kofin zakarun Turaida kuma shekaru biyu da ya yi da kungiyar Schalke 04.
Karim Benzema - Kwallaye 90
A shekaru 18 da haihuwa dan wasan Faransa ya jefa kwallon farko a wasannin cin kofin zakarun Turai a farko da kungiyar Lyyon. Daga shekara ta 2009 zuwa 2023, Benzema yana cikin wadanda suka yi fice har zuwa kungiyar Real Madrid. Bayan karya yatsa a shekara ta 2019 Benzema yana wasa yatsa a daure, sannan akwai jita-jita game da lafiyarsa. A shekara ta 2023 ya bar Turai zuwa Saudiyya.
Robert Lewandowski - Kwallaye 96*
Tsohon dan wasan kungiyar Bayern Munich wanda ya lashe gasar a shekara ta 2020 yana cikin fitattun 'yan wasa na duniya, kuma wanda yake kan gaba wajen jefa kwallaye a wasannin neman cin kofin zakarun Turai. Ya yi wasa da kungiyoyin Borussia Dortmund, FC Bayern da FC Barcelona. (Wannan har zuwa daya ga watan Oktoba na shekara ta 2024).
Lionel Messi - Kwallaye 129
Idan kungiyar FC Barcelona za ta dogara da wani tsakanin shekara ta 2004 zuwa 2021 , zai zama Lionel Messi wanda ya kware wajen jefa kwallo a raga. Dan Ajentina ya jefa kwallaye 120 tare da Barcelona a wasannin cin kofin zakarun Turai, ya yi wasa na wani lokaci da kungiyar PSG. Dan wasan sau shida ya zama wanda ya fi cin kwallaye a wasannin cin kofin zakarun Turai. Yana Amurka tun shekara ta 2023.
Cristiano Ronaldo - Kwallaye 140
Dan wasan daga kasar Potugal ya lashe gasar zakarun Turai sau biyar. Duk wuraren da ya yi wasa daga Manchester United, Real Madrid or Juventus Turin, shi dai Cristiano Ronaldo ya zama wanda yake jefa kwallaye a raga. Sau biyar ya zama kwarzon 'yan wasa na duniya, wanda zai kawo karshen wasannin da yake a kasar Saudiyya. Ya zama wanda ya fi kowa jefa kwallaye a wasannin cin kofin zakarun Turai.