Kamaru: Yadda ake kallon shugabancin Paul Biya
February 13, 2023Shugaba Paul Biya na Kamaru ya cika shekaru 90 da haifuwa. Biya shi ne shugaba kasa mafi tsufa a duniya wanda kuma yanzu haka muhawara ta kaure a kasar ta Kamaru kan cewar ba shi da cikakken kuzari yin jagorancin kasar.
Birnin Younde ya dauki harami da hotunan Shugaba Paul Biya wanda wasu 'yan Kamaru ke yi wa kallon jarumi wasu kuma na yi masa kallon kasashe. Bikin na cikar shekaru 90 da haifuwar Paul Biya na zuwa ne daf da lokacin da ake yin bukukuwan ranar da aka ware ta musammun ta matasa a Kamaru wadanda suke jinjinawa shugaban.
Paul Biya mai shekaru casa'in a duniya, ana yi masa kallon shugaban kasa mafi tsufa da ya dade a kan karagar mulki shekaru 40 wanda ya ci jiya, ya ci yau, har ma yana hangen badin badada duk da irin yadda tsufa ya bada masa yaji.
A Kasar ta Kamaru babu wanda ya aminta cewar Paul Biya shi ke shugabancin kasar saboda ana ganin iyalansa da na kusa da shi sune ke tafiyar da mulkin sai abin da aka rawaito masa. Fadawa da wasu kusoshi gwamnatin na ganin tafiyar a haka ta fiye musu kyau a bi yarima a sha kida ko da ko akwai bukatar samun sauyi na shugabanci. Amma duk da haka wasu 'yan Kamarun na cewar shugaban abin godiya ne.
Sai dai masu yin adawa da gwamnatin ta Biya na cewa, duk da shekaru 40 da ya yi a kan mulki ya gaza gyar wasu al'amuran kasar na tattalin arziki da zamantakewa da ma gaza sasanta rikicin 'yan Ambazoniya masu magana da harshen Ingilishi sannan a baya-baya nan, akan samun yawan kashe-kashe na farar hula wadanda suka hada da wani dan jarida Martinez Zogo da kuma wani ma'akacin gwamnatin da aka kashe a ranar Jumma'ar da ta gabata.
Paul Biya wanda shi kam karfinsa ya rika ya kare kan mulki ana tunanin cewar babban dansa Emmanuel Franck Biya zai iya gadonsa idan har ta Allah ta kama. Sai dai yaya makomar kasar za ta kasance.