SiyasaJamus
Siriya: Ziyarar wakilan Jamus da Faransa
January 3, 2025Talla
Ministar harkokin kasashen ketaren ta Jamus Annalena Baerbock ta bukaci a hukunta tsofafin jami'an rusasshiyar gwamnatin kama-karya ta Siriya karkashin jagorancin Bashar al-Assad ne, a Damascus babban birnin kasar ta Siriya yayin da ta ziryaci gidan kurkukun Sednaya da ke birnin na Damascus da aka bayyana da sansanin azabtarwa da kisan 'yan adawa na Assad. Baerbock na ziyara ne da takwaranta na Faransa Jean-Noël Barrot a madadin kungiyar Tarayyar Turai, inda aka nuna musu duka wuraren da ake gana azaba cikin gidan kason na Sednaya. A cewarta, tilas a ci gaba da taimakon kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ke kasar. Ministocin kasashen ketaren na Jamus da Faransa, za su gana da gwamnatin rikon kwaryar ta Siriya.