Shirin yi wa matsalar tsaron yankin Sahel taron dangi
March 23, 2023Wakilan kasashe kusan 50 sun hallara a binin Brussels na kasar Beljiyam domin tattaunawa kan kara hadin gwiwa a fannin tsaro a daidai lokacin da Turai ke sake duba muhimman abubuwan da ta sa a gaba, yayin da ake fama da yakin Ukraine. ministan tsaro na Nijar Alkasoum Indatou na daga cikin wadanda suka halarci taron na yin bita dangane da tallafin da MajalisarTarayyar Turai ke bai wa kasashen a fannin tsaro a karkashin wani tsari na hadin gwiwa a kasashe dabam-dabam.
Tun farko bisa bukatar mahukuntan Nijar, Majalisar Tarayyar Turai ta kaddamar da wani shirin hadin gwiwa na soji da kasar Nijar, mai suna EUMPM Niger. Makasudi shirin shi ne karfafa karfin sojojin Nijar wajen yaki da ta'addanci. Tawagar hadin gwiwa da aka kafa a hukumance a ranar 12 ga watan Disambar 2022 bisa bukatar hukumomin na Nijar, na da kuma munufar kare al'ummar kasar da tabbatar da yanayi mai aminci da tsaro tare da mutunta hakkin dan Adam.
EUMPM Nijar za ta ba da goyon baya musamman wajen samar da cibiyar horar da kwararrun sojoji, da bayar da shawarwari tare da tallafawa wajen samar da sabuwar bataliya soji ta musammun domin yaki da ta'addanci. A taron da Majalisar Tarayyar Turai ta kira a Brussels tare da wasu sauran kasashen, za a yi bita na irin bukatun da kasashen suke da ita a fannin tsaro a kokarin da ake yi na yakar ta'addanci a yankin Sahel.
Wannan shiri da aka kaddamar zai kammala a tsawon shekaru uku kafin sake sabunta shi, adadin kudaden da za a kashe a cikin wannan lokacin zai kai Yuro miliyan 27.3. Tun daga shekarar ta 2012, yankin Sahel ke fuskantar matsalar tsaro mai zurfi wadda ta janyo cikas a kan harkokin tattalin arziki. Nijar na daga cikin kasashen da ke cikin matsalar da ke kokarin neman mafita tare da sauran kasashe abokanan hulda.
.