Wakilin Majalisar Dinkin Dunia a gabas ta tsakiya ya bayana damuwa a kan halin da yankin ke ciki
July 4, 2006Wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin gabas ta tsakiya, ya bayana damuwa, a game da tabarbarewar zaman lahia tsakanin Isra´ila da Palestinu, bayan sace sojan Isra´ila da wasu dakarun sari ka noƙen Palestinawa su ka yi.
Alvarato de Soto, ya ce ko kamin faruwar al´amarin yankin gabas ta tsakiya ya kasance gurbatace, to amma a halin da ake ciki, tashin hankalin ya kai intaha.
A yunkurin da ta ke na gano sojan ta ta ko wane hali, Isra´ila na ci gaba da kai hare ahren a zirinGaza, tare da jawo assara mai tarin yawa.
Ranar 28 ga watan da ya gabata, rundunar Isra´ila ta tarwatsa wata cibiyar samar da wutar lantarki,a zirin Gaza.
A sakamakon haka, mazauna yankin, sun faɗa cikin matsanancin hali ,na rashin tsabtattun ruwan sha,da kuma karancin wutar lantarki.
Bugu da ƙari cuttutuka iri-iri sai ƙara yaɗuwa su ke.
Alvaro de Soto ya bayyana adawar Majalisar Ɗinkin Dunia, a game da matakin da gwamnatin Isra´ila ta ɗauka, na capke ministoci da kuma yan majalisun dokokin Hamas.