1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

wakilin Rasha ya baiyana shakku game da samarda kuria yau kan batun Iran

December 22, 2006
https://p.dw.com/p/BuWh

Akwai alamun cewa ba zaa iya samarda kuria ba kan shirin nukiliya na Iran a yau jumaa bayan ganawar komitin sulhu akan wannan batu.

Zaunnannun membobin komitin sulhu na majalisar dinkin duniya su 5 da Jamus,sun kammala tattaunawa ba tare da samar da kudirin karshe ba akan shirin nukiliya na kasar Iran.

Bayan ganawa tsakanin jakadun kasashen Amurka da Rasha,Faransa,Burtaniya,Sin da kuma Jamus,wakilin kasar Rasha Vitaly Churkin ya baiyana cewa har yanzu akawai wasu batutuwa guda 2 zuwa 3 da baa cimma matsaya a kansu ba.

Churkin yace,yana sa zuwa gobe asabar zaa samu jefa kuria kann shwarawari da aka yanke.

Kasashen Jamus Faransa da Burtaniya suka bada shawarar kafa takunkumin tafiye tafiye da kuma dakatar da kadarorin Iraniya da suke da hannu a shirin nukiliya na kasar.