2025: Kalubalen dimukuradiyya a Afirka
January 2, 2025Masu lura da al'amuran na ganin duk da bunkasar tattalin arziki da aka samu a wasu kasashen Afirka, kalubalen da ke da nasaba da talauci da basussuka da kuma rikice-rikicen makamai zai ci gaba da yin tasiri a nahiyar. Farawa da babban zaben Mozambique, inda masu lura da harkokin siyasa ke fargabar za a ci gaba da tashe-tashen hankula. Zaben shugaban kasa na watan Oktobar shekara ta 2024 da ta gabata, ya haifar da zanga-zanga daga magoya bayan fitaccen dan adawa nan Venâncio Mondlane da suka zargi jam'iyyar FRELIMO mai mulki da magudin zabe.A cewar Serwah Prempeh ta Cibiyar Bincike kan Manufofin Afirka (APRI), raguwar dimukuradiyya a yawancin kasashen Afirka ya kasance abin damuwa. Ga misali a kasar Tunisiya da Mauritaniya da suka dauki matakai na tabbatar da dimukuradiyya na kan hanya, amma dai zabubbukansu sun fuskanci kura-kurai.
A shekara ta 2024 da ta shude, an gudanar da zabuka masu muhimmanci da dama musamman a kasashen Mauritius da Botswana da Senegal. An samu sauyi cikin lumana a Afirka ta Kudu,daga jam'iyya mai mulki zuwa gwamnatin jam'iyyun hadaka. A cewar bankin duniya ana sa ran tattalin arzikin kasahen yankin Kudu da Sahara zai habaka da kaso hudu cikin 100 nan da shekarar ta 2025, wanda zai samu goyon bayan kasuwanci da zuba jari da sauye-sauye na zamani. Bayan Afirka ta Kudu ana sa ran kasashe masu karfin tattalin arziki kamar Najeriya da Kenya za su ci gaba da samun ci-gaba mai dorewa, yayin da kasashe masu tasowa kamar Ruwanda da Habasha ke kara samun ci-gaba. Yammacin Afirka da yankin Sahel, na ci gaba da fuskantar koma-baya a siyasance. Juyin mulkin da soja suka yi a Nijar da Mali da Burkina Faso da Guinea, na yin barazanar shafe nasarorin dimukuradiyya. Har ila yau, ta'addancin kungiyoyi masu jihadi na ci gaba da yin illa ga tsaro da gudanar da zabe a wadannan yankuna a shekara ta 2025.