Jana'izzar 'yan matan da suka mutu a Kabul
May 9, 2021Talla
Rahotanni sun ce dangi da iyayen yara 'yan makaranta da suka mutu na ci gaba da kasancewa cikin dimuwa, bisa harin da ya halaka daliban, wanda kuma ke zaman irinsa mafi muni da aka kaddamar kasa da shekara guda kan wata makaranta a kasar Afghanistan.
Baya da 'yan mata da suka mutu, wasu fiye da 100 suka jikkata sakamakon wasu tagwayen fashewar bama-bamai a makarantar Sayyedil Shuhada da ke unguwar mabiya mazhabar Shi'a ta binin Kabul.
Tuni dai hukumomi a kasar ta Afghanistan suka zargi kungiyar Taliban da wannan aika-aikar.