Wani hari ya jikkata dakarun MDD a Mali
May 6, 2023Talla
Cikin wani sakon da ta wallafa a shafukan sada zumunta, rundunar MINUSMA da ke tabbatar da zaman lafiya a Mali ta ce wadanda harin ya ritsa da su na samun kulawar da ta dace, ba tare da bayyana halin da suke ciki da kasashensu ba.
Wannan dai shi ne harin bam ko nakiya na shida da aka kai a shekarar 2023 a tsakiyar kasar Mali, da ke zama tungar masu ikirarin jihadi da tashe-tashen hankula, lamarin da ke haddasa zubar da jini a kasar da ke yankin Sahel.
Ita dai Minusma mai sojoji kusan 12,000, ita ce tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta fi fama da asarar rayuka mafi yawa a duniya a 'yan shekarun nan, inda membobinta 185 suka mutu a cikin shekaru 10.