Wani harin ƙunar baƙin wake a arewa maso yammacin Pakistan ya halaka soji 24
July 15, 2007Talla
Kwanaki 3 bayan dirar mikiya da jami´an tsaron Pakistan suka yiwa Masallacin Red Mosque dake birnin Islamabad, wani dan kunar bakin wake ya halaka sojoji akalla 24 sannan ya jiwa 29 raunuka. Wani kakakin rundunar sojin kasar ya ce a jiya asabar dan kunar bakin wake ya ta dana bama-bamai da ya cika su a cikin wata mota akan wani ayarin motocin sojoji a yankin arewa maso yammacin kasar. Masu kishin Islama a wannan yanki dake kan iyaka da Afghanistan sun yi kira da a dauki fansa bayan da hukumomin Pakistan suka afkawa masallacin na Red Mosque dake Islamabad. Alkalumman baya bayan nan da kafofin yada labaru suka bayar sun mutane 102 suka rasa rayukansu ciki har da ´yan takife 60 a fito na fiton da aka yi a masallacin.