Wani harin bam ya hallaka mutane a Pakistan
January 30, 2015Talla
A kalla dai mutane 40 ne suka rasu yayin da wasu gwammai suka jikkata bayan harin da aka kai a daidai lokacin da mutane ke cikin Sallar Jumma'a a kudancin birnin Shikarpur da ke a nisan a kalla km 500 da birnin Karashi da ke a matsayin babban birnin Jihar Sind a kasar ta Pakisatan.
Ministan kiwon lafiyar wannan yanki Jam Mehtab Daher, ya sanar cewa a kalla mutane 40 ne suka rasu wasu kuma kusan 50 suka jikkata inda ya ce kuma wannan adadi na iya karuwa nan gaba. An samu gano gawawakin mutane da dama da aka iya tantancesu, yayin da wasu gawawakin suka kone kurmus a cewar ministan da ma wasu majiyoyin asibitin birnin Shikarpur.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba