1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jirgin saman fasinja ya bace a Nijeriya bayan tashinsa daga Legas

October 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvOG

Jiragen sama masu saukar ungulu na sojin Nijeriya sun nemi wani jirgin saman fasinja dauke da akalla mutane 114 ya bace jim kadan bayan tashinsa daga Legas cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriya akan hanyarsa ta zuwa Abuja. Kakakin hukumar kula da filayen jiragen sama a Nijeriya Jide Ibinola ya ce an daina jin duriyar jirgin ne samfurin boeing 737 mallakin kamfanin Belview Airlines kimanin mintuna biyar bayan ya tashi daga babban filin jirgin saman Legas da misalin karfe 8 na daren jiya asabar agogon Nijeriya. Gidan telebijin kasar dai ya rawaito cewa matukan jirgin saman sun ce sun shiga wani mawuyaci hali kafin jirgin ya bace daga allon raeda ta masu sarrafa zirga-zirgar jiragen saman a yamma da birnin na Legas. Ibinola ya ce jiragen sama masu saukar ungulu na soji da aka tura don nemo jirgin dai sun koma sansanonin su ba tare da wata nasara ba. Wakliyar mu a jihar Jigawa ta rawaito cewa gidan telebijin Nijeriya ya tabbatar da faduwar jirgin ko da yake har yanzu hukumomin kasar ba su tabbatar da haka ba.