1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye sun hallaka mutane da dama a Kwango

Mohammad Nasiru Awal AH
November 27, 2019

An zargi 'yan tawayen kungiyar Allied Demorcatic Forces da ke da sansanin a kasar Yuganda da kai harin. Fiye da mutane 1500 'yan tawaye suka kashe a tsukin shekaru hudu a ciki da wajen birnin Beni.

https://p.dw.com/p/3Tqkg
'Yan kungiyar ta Allied Demorcatic Forces sun sha kai hare-hare a gabacin Kwango
'Yan kungiyar ta Allied Demorcatic Forces sun sha kai hare-hare a gabacin Kwango Hoto: DW/J. Kanyunyu

Wani jami'i a gabashin jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya ce fiye da mutum 12 'yan tawaye suka kashe a wani sabon hari da suka kai kusa da birnin Beni, inda a wannan mako mazauna suka farma wani sansanin Majalisar Dinkin Duniya don neman a ba su kariya.

Kantoman yankin Beni, Donat Kibwana ya ce an kai harin ne a cikin dare a garin Oicha. Ya zargi 'yan tawayen kungiyar Allied Demorcatic Forces da ke da sansanin a kasar Yuganda da kai harin.

Fiye da mutane 1500 'yan tawaye suka kashe a tsukin shekaru hudu a ciki da wajen birnin Beni.

A wani labarin kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce fiye da mutum 5000 cutar kyanda ta yi sanadin ajalinsu a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a wannan shekara. Adadin dai ya ninka har sau biyu a kasar da ke fama da annobar Ebola.

Hukumar ta WHO ta ce lamarin a Kwango shi ne mafi muni a duniya baki daya, inda kawo ranar 17 ga watan nan na Nuwamba aka yi rajistar mutum fiye da dubu 250 da suka kamu da kyanda yayin da 5110 suka rasu sakamakon cutar.