Wani yankin da ke hannun Al-shabab ya koma hannun gwamnati
July 23, 2015Dakarun Somaliya da Kungiyar Tarayyar Afirka sun yi nasarar anshe wani gari da ke yankin kudu maso yammacin kasar, daya daga cikin yankunan karshe da kungiyar Al-shabab ke cin karenta ba babbaka a yankin kahon Afirkan.
Shaidu sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran Jamus cewa dakarun sun dira kasar ne tare da manyan tankokin yaki da jirage masu saukar ungulu.
Ana dai kyautata zaton cewa kwace wannan yanki zai yi tasiri kan harkokin kungiyar ta Al-shabab, saboda baya ga amfani da shi a matsayin makarfafanta, aiyukan noma na da inganci, kuma ya kasance musu hanyar samun kudi, inda bayan nan kuma suke dorawa da karbar haraji da karfi da yaji daga mazauna yankin.
Tun shekara ta 2007 dakarun Kungiyar Tarayyar Afirka ke kasar Somaliya domin dafa wa dakarun a yakin da suke yi da kungiyar Al-shabab, kuma a yanzu haka adadinsu ya kai dubu 20.