Wannan yanki ya raba Koriya ta Arewa da ta Kudu
Shiga wasannin Olympics na lokacin hunturu a yankin Pyeonchang na Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa ta yi, ya ba da kyakkyawan fata. Amma har yanzu akwai tsakani daidai da iyakarsu mai tsawon kilomita 248.
Ba hanyar shiga Koriya ta Arewa
Tun shekaru 65 aka raba yankin tsibirin Koriya zuwa Koriya ta Arewa da ta Kudu. Bayan yakin Koriya na shekaru uku a 1953 aka kirkiro da yankin da aka hana aikin soji a cikinsa wato DMZ. Iyakar mai tsawon Kilomita 248 ta tashi daga Kudu maso Yamma zuwa Arewa maso Gabas tana da fadin Kilomita hudu. Sojojin Koriya ta Arewa ke sintir a wannan titin da ke da kusa da yankin DMZ.
Katangar wayar karfe
A hana girke sojoji a cikin yankin da ba a aikin soji. Wata hukumar tsagaita bude wuta da ke da wakilai daga bangarorin biyu ke kula da yankin na DMZ. Ba a shiga yankin sai da izinin wannan hukuma. A kan yi harbe-harbe a gabar tekun don tsoratar da masu karya doka.
Gidaje masu launin shudi
Mazaunin hukumar tsagaita wutar yana a Panmunjeom a cikin yankin na DMZ. Daga 1951 zuwa 1953 aka kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin Koriya. A tsakanin barikokin guda uku masu launin shudi, aka shata layin iyakar tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu. Kowane daga cikinsu na da kofa daya daga bangaren Koriya ta Arewa da ta Kudu.
Gida guda, kasashe biyu
Ana bayayyar bude barkin da ke tsakiya ga maziyarta daga bangarorin biyu. Sojojin kasar da za a shiga bangarenta na dakin, su ke gadin kofar daya kasar Koriya. Sai dai a cikin kananan dakunan ne ake yarda a tsallake kan iyakar.
Hango Koriya ta Arewa cikin sauki
A yankin na DMZ an yi ta samun rikice-rikice da kai hari da ma kisa. Amma Koriya ta Kudu ta yi babbar nasarar samun filin iyaka mai girma saboda muradu na kasar da ma duniya baki daya. Hasumiyar sa ido kan sake hadewar yankunan da ke kusa da birnin Goseong na ba da damar hango makociyar kasa Koriya ta Arewa tun daga katangar wayar.
Jan hankalin masu yawon bude ido
Dandamalin hangen nesa na ba da damar hangen yankin da aka hana aikin soji, wanda kuma ke zama bain sha'awa ga masu yawon bude ido. A 2015 mutane kimanin miliyan 13,2 suka kai ziyara Koriya ta Kudu. Da yawa daga cikinsu sun yi amfani da madubin hangen-nesa sun ga yanayin shimfidar kasar Koriya ta Arewa.
Kilogram 270 na kishin kasa
A bangaren Koriya ta Arewa na yankin DMZ akwai kauyen Kijŏng-dong. A da daga wurin ake yada farfagandar Koriya ta Arewa tan amfani da amsa kuwa. Babbar alama ta Kijŏng-dong ita ce hasumiyar na mai tsayin Mita 160, da ke zama na hudu mafi tsayi a duniya. A samarta aka kafa tutar Koriya ta Arewa mai nauyin Kilogram 270.
Bore na launuka dabam-dabam
Ko da yake ba a aikin soji a yankin kasashen biyu, amma daukacin Koriyawa na neman zaman lafiya mai dorewa. Kamar a "Dandalin zaman lafiya na Imjingak" a Paju da ke Koriya ta Kudu a kusa da yankin DMZ. Kyalluna masu launuka aka daure a kan wayoyin kaya na zama bukatar ganin an sake hade kasashen biyu tare kuma da samun zaman lafiya.
So da kauna da kuma zaman lafiya
Hatta a kusa da hasumiyar sa ido kan sake hadewa da ke Koriya ta Kudu ana fatan magance rikicin. A kan manyan haruffan an yi rubuce-rubuce da kalmomin "So" da "Kauna" da "Zaman Lafiya" a cikin harsuna dabam-dabam.