1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasan karshe na cin kofin duniya

July 12, 2010

Kasar Spain ta dauki kofin kwallon kafa na duniya

https://p.dw.com/p/OGlB
Yan wasan Spain tare da kofin duniyaHoto: AP

Ranar Lahadi a birnin Johannesburg aka kawo karshen wasannin kwllon kafa jna cin kofin duniya da aka yi makonni hudu ana gudanarwa a Afrikata kudu.

Wannan abin mamaki ne, abin da bamu taba zato ba. Wannan wasa ya dauki kwashe karfin mu gaba daya, kuma bai zama mai sauki garemu ba. To amma babu abin da za'a iya kwatanta shi da nasarar daukar kofin duniya.

Wannan dai shine yadda Andres Iniesta ya baiyana nasararda kasar sa ta samu a wasannin na cin kofin duniya a bana.

Mai abu dai ya dauki abu nai. Bayan wasnani na tsawon kwanaki talatin, bikin gasar wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya a Afirka ta kudu ya shiga kundin tarihi. Ranar Lahadi da yamma ne aka gudanar da wasa na 64 da hudu kuma na karshe, a gasar ta shekara ta 2010, inda Spain, dake rike da kofin Turai ta kara da Holland. Duka wadannan kasashe biyu dai basu taba daukar kofin na duniya ba, kuma ga kasar Spain ma, wasan na ranar Lahadi shine na farko a gare ta a matsayin wasan karshe, na neman daukar kofin duniya. A wasan kuwa tayi rawar gani domin bayan minti casa'in da karin lokaci na minti talatin, kasar ta Spain ta sami nasara kan Holland daci daya ba ko daya. Hakan ya sanya Holland a karo na ukku, bayan shekara ta 1974 da shekara ta 1978, ta koma gida daga wasnanin cin kofin duiya tareda lambar azurfa a matsayi na biyu.

Wasan karshe da aka yi a jiya, kamar yadda masana masu yawa suka nunar, bai cancanci a kira shi waan karshe ba, saboda rashin sha'awa ga yan kalo. Duk da haka dai, kasashen biyu sun yi ta kai wa junan su kora a duk tsawon lokacin da suka samu. Bayan minti arba'in da biyar an tafi hutun rabin lokaci babu inda aka ci. A rabi na biyu, ko wacce ta sami damar jefa kwallo a gidan abokan karawa, amma bayan minti casa'in ya zama tilas sai an kara lokaci na minti talatin. Minti uku kafin wannan karin lokaci ya cika, dan wasan gaba na Spain, wato Andres Iniesta ya jefa kwallo a gidan yan wasan Holland, kuma aka tashi Spain taci daya, Holland tana nema. Bayan wasanni biyu da bata sami nasara ba, Holland ta shiga fili ne a jiya da niyyar daukar wannan kofi karo na farko. Dan wasan kasar, Nigel de Jong, ya baiyana bakin cikin sa a game da rashin nasara a wasan na jiya.

"Yace a yau mun yi iyakacin kokarin mu don mu sami nasara, amma hakan bai samu ba, musmman kudirin da alkalin wasa ya dauka da ko kadan bai dace ba. To amma dama haka wasan kwallon kafa yake. Wajibi ne mu nuna karfin zuciya mu hangi gaba".

Spain din dai ta sanya tarihi a fannoni da dama sakamakon nasarar ta, ta daukar kofin duiya a filin wasa na Soccer City, gaban yan kallo dubu 84. Wannan dai shine karo na farko da kasar ta dauki kofin duniya, kuma ta zama kasa ta takwas a jerin wadanda suka taba daukar kofin duniya a tarihin sa na shekaru tamanin. Kasar wannan shine karon farko da ta kai wasan karshe, kuma ita ce kasa ta farko daga nahiyar Turai da ta dauki kofin duniya a wasnnin da aka yi ba a nahiyar Turai din ba.

A karshen wasannin, shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Joseph Blatter yace:

"Nahiyar Afrika tana iya alfaharin samun nasarar tsara wadannan wanni na cin kofin duniya".

Ga kasar Spain wasannin na bana sun zama abin alfahari, ba ma gare ta kadai amma har ga nahiyar Turai ganin cewar bayan Italiya shekaru hudu da suka wuce, kofin na duniya zai zauna a nan Turai tsawon wasu shekaru hudu masu zuwa.

Maawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Zainab Mohammed Abubakar