1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kofin zakarun Turai a yanayin corona samfarin Delta

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
July 11, 2021

Ana fargabar yaduwar sabon nau'in Delta na cutar corona a Birtaniya, a daidai lokacin da ake shirin buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na 2020 a tsakanin Italiya da Ingila.

https://p.dw.com/p/3wKRV
Fußball EM | England v Dänemark | Fans
Hoto: Frank Hoermann/SVEN SIMON/imago images

Ingila wacce ta yi ba zata a gasar cin kofin dai za ta kece raini da takwarata ta Italiya a gaban 'yan kallo fiye da dubu 60 a filin wasa na Wembley da ke kusa da birnin Landan.

Daruruwan magoya bayan kungiyar Ingila na cike da zumudin ganin yadda wasan zai kasance, inda suka yi dandazo a dab da filin wasan Wembley suna rera wakoki da shan barasa, tare da fatan ganin kasar ta dau kofin wanda ta yi wa bankwana tun a shekarar 1966.

Sai dai ana nuna damuwa kan yadda annobar corona nau'ilnDelta mai saurin yaduwa, ka iya yin tasiri a bukukwan karshen wasan na cin kofin zakarun Turai.