1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Euro 2024: Spain da Ingila, za su yi karon batar karfe

Mouhamadou Awal Balarabe AH
July 11, 2024

Aski ya iso gaban goshi a kokarin da kasashen Turai ke yi na lashe kofin kwallon kafar wannan nahiya a gasar da ke gudana a Jamus, inda Spain za ta kara da Ingila a wasan karshe.

https://p.dw.com/p/4iAeA
Fußball-EM 2024 | Halbfinale | Spanien vs. Frankreich | Lamine Yamal erzielt Tor für Spanien
Hoto: Manuel Blondeau/AOP.Press/IMAGO

 Wannan jadawalin ya kammala ne bayan da Three Lions ta Ingila ta yi nasarar doke Holland a wasan kusa da na karshe a birnin Dortmund.

UEFA Euro 2024: Spanien - Frankreich
Hoto: Ariel Schalit/ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Babu sigar da Ingila da Holland ba su gani ba a wasan kusa da na karshe da su buga a birnin Dortmund na yammacin Jamus, kama daga kwallon da ya bi saman tirke bayan ya kauce ma raga, har i zuwa ga kauce ma sakiyar da babu ruwa da masu tsaron gida suk yi. Amma abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda Xavi Simons na Holland ya zura kwallo a ragar Ingila bayan shafe mintuna bakwai da fara wasa. Wannan ne ya sa 'yan wasan Three Lions farkawa daga barci tare da matsa wa 'yan Netherlands lamba, lamarin da ya kai su ga samun bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da Denzel Dumfries ya yi keta a yadi na 18. Shi kuwa Harry Kane wanda yake buga wa Bayern Munich kwallo ya zura kwallo a raga a minti na 18 da fara wasa.

Fußball Euro 2024 | Niederlande v England
Hoto: Darko Vojinovic/AP/picture alliance

Daga bisani, 'yan wasan na Ingila sun ci gaba da yunkurawa, amma suka kasa ninka kwallon da suka zura, musamman ma lokcin da Phil Foden ya buga kwallo da ya bugi tirke, hakan ya ba wa Dumfries damar ceto kungiyarsa daga raraka. Sai dai hasken Ingila ya zo ne daga karshe daga Ollie Watkins dan wasan Aston Villa, wanda ya maye gurbin Harry Kane da aka fitar daga filin daga, inda ya yi amfani da kwallo da Cole Palmer ya mika masa, na da nan kuwa ya shammaci mai tsaron gida Bart Verbruggen kafin a yi busan karshe.

UEFA Euro 2024: Spanien - Frankreich
Hoto: Bradley Collyer/empics/picture alliance

Wannan ci 2-1 ya ba wa Ingila damar tsallakawa zuwa wasan karshe na gasar Euro a karo na biyu a jere. Amma a wannan karon, Harry Kane da abokan wasansa suka ce ko ana ha maza ha mata za su lashe gasar ta Euro 2024: "Muna samun ci gaba a kowane zagaye. Ina ganin cewar bajintarmu na nuna ci-gaban da muka samu wannan shi ne mafi kyawun wasanmu na gasar Euro, mun cancanci wannan nasarar. Na fahimci muhawara da ake yi game da salon wasanmu, amma ko yaushe ina fada cewar ya kamata a yi mana hukunci bayan gasar Euro 2024,  dole ne a bar mu mu gama abin da muka sa a gaba. Muna alfaharin kasancewa a wasan karshe, amma a gaskiya mun zo nan ne domin lashe wannan gasa. Za mu sha wahala a karawa da Spain, amma abu kadan ya rage mana don mu kafa tarihi."