1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kevin-Prince Boateng zai tantance makoma a kwallo

Suleiman Babayo AMA
July 3, 2023

An yi nisa a gasar neman cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka 'yan kasa da shekaru 23 kana an kawo karshen tseren motocin Formular One.

https://p.dw.com/p/4TMJv
Matasan Najeriya na kwallon kafa
Matasan Najeriya na kwallon kafaHoto: Shaun Roy/BackpagePix/empics/picture alliance

Kevin-Prince Boateng daya daga cikin fitattun 'yan wasa na gasra Bundesliga  zai bayyana matakin da ya dauka cikin makoanni biyu masu zuwa na ci gaba da wasa ko kuma yin ritaya, yayin da kwantriraginsa ke kawo karshe da kungiyar Hertha Berlin wadda ta fice daga gasar Bundesliga ta koma matsayi na biyu a wasannin kwararru na Jamus. Tun shekara ta 2005 Kevin-Prince Boateng ya fara wasannin kwararru daga kungiyar ta Hertha inda ya sake komawa kungiyar a shekara ta 2021, bayan da ya yi wasu kungiyoyi da suka hada Tottenham Hotspur ta Ingila, da AC Milan ta Italiya, da Schalke da Frankfurt duk anan Jamus.

Fussball, Herren, Saison 2022/2023, 1. Bundesliga (33. Spieltag), Hertha BSC - VfL Bochum, Kevin Prince Boateng (Hertha
Kevin Prince Boateng dan wasan Hertha BerlinHoto: IMAGO/Matthias Koch

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na  Afirka na matasa ‘yan kasa da shekaru 23 da ke gudana a kasar Maroko, aski ya fara kawo gaban goshi inda a yanzu aka san kasashe hudu da suka samu tikitin buga wasan kusa da na karshe.  Sai dai duk da yake cewa Nijar na daga cikin jerin kasashen da suka kasa ketara siradi a gasar, kwararru a fannin kwallon kafa na bayyana gamsuwarsu dangane da yadda sannu a hankali masu horas da ‘yan wasa na cikin gida ke samun nasara fiye da wadanda kasar ke daukowa daga kasashen Turai.

'Yan Wasan Moroko da Aljeriya
'Yan Wasan Moroko da AljeriyaHoto: Shaun Roy/Sports/empics/picture alliance

Bayan buga wasanni uku-uku a cikin rukunnai guda biyu na gasar cin kofin kwallon kafar ta Afirka ta matasa ‘yan kasa da shekaru 23, kasar Masar mai rike da kofin da Maroko mai masaukin baki da Mali da kuma Guinea sun samu tikitin zuwa wasan kusa da na karshe. Maroko ta zo ta farko ne a rukuninta da maki tara bayan da ta doke Guinea da ci biyu da daya, ta sarrafa Ghana da ci biyar da daya ta sha Jamhuriyar demokradiyyar Kwango da ci daya mai ban haushi, a yayin da daga nata bangare Masar ke a sahun gaban rukuninta da maki bakwai bayan da ta tashi ba kare bin damo banza-da banza tsakanina da Nijar ta doke Mali da ci daya mai ban haushi, ta kuma casa Gabon da ci biyu da nema. Guinea ta kai zagayen kusa da na karshe da maki hudu bayan da ta doke  Jamhuriyar demokradiyyar Kwango da ci 3-1, ta kuma yi kunnan doki da Ghana daya da daya, sai kuma Mali wacce ta samu tikitin bayan da ta doke Gabon da ci 3-1 ta kuma lallasa Jamhuriyar Nijar da ci biyu da babu wanda ya yi dalilin fitar da Nijar daga gasar.

A wasanin Tennis, ana sa ran girmama Roger Federer gobe Talata yayin da ake ci gaba da gasar Wimbledon saboda irin rawar da ya taka a gasar na Ingila cikin shekarun da suka gabata. Shi dai Roger Federer dan Switzerland sau takwas yana lashe gasar mai tasiri, inda a watan Satumba ya bayyana yin murabus daga wasa.

'Yan wasan Siri Lanka
'Yan wasan Siri Lanka na CricketHoto: PUNIT PARANJPE/AFP

Kasar Siri Lanka ta samu nasarar kai wa zuwa gasar neman cin kofin Cricket ta duniya da za a gudanar cikin wannan shekara ta 2023. Siri Lanka ta tsallaka sakamakon doke kasar Zimbabuwe a wasan da aka yi a karshen mako. Yanzu haka Zimbabuwe za ta iya tsallakawa idan ta samu nasara kan Scotland a wasa da zai wakana a wannan Talata. A watan Oktoba mai zuwa kasar Indiya za ta dauki nauyin gasar ta Cricket ta duniya.

Max Verstappen ya lashe gasar tseren motocin Formula One da aka kammala a Austriya,  inda ya tsallake rudanin da aka fuskanta tun farko, abin da ke zama gagarumin mataki a wasan na Formula One. Verstappen yana cikin wadanda suka mamaye gasar tseren motocin na Formula One. Haka Sophia Flörsch 'yar kasar Jamus ta zama mace ta farko da ta samu maki a gasar tseren motoci da ya gudana a wannan Lahadi da ta gabata a Austriya, kuma ta nuna farin ciki da haka. 'yar shekaru 22 da haihuwa ita dai Sophia Flörsch ta samu makin lokacin gasar.