Takun saka tsakanin Aljeriya da Maroko
January 9, 2023Ya zuwa yanzu dai kasashe biyar ne suka shigar da takarda a hukumance ga Hukumar Kwallon Kafa ta AFirka CAF da ke birnin Alkahira, wadanda suka hada da Aljeriya da Maroko da Zambiya da kuma Najeriya da Benin. Bayan kammala ziyarar duba filayen kwallo da sauran kayan da za a bukata da aka fara daga ranar biyar zuwa 25 ga wannan wata na Janairu ne, kwamitin zartaswa zai sanar da kasar da za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta Afirka a ranar 10 ga watan Fabrairun da ke tafe. Hukumar ta CAF dai, ta bar kofa a bude ga hadin gwiwa tsakanin kasashe da dama don shirya gasar ta AFCON. Idan dai ba a manta ba, hukumar kwallon kafa ta Afirka ta janye gasar AFCON ko CAN ta 2025 daga hannun Guinea Conakry a watan Oktobar bara, saboda ana ganin kasar ba ta shirya ba wajen samar da ababen more rayuwa da za su bayar da damar daukar nauyin gudanar da wannan gagarumin biki a kwallon kafar Afirkan.
Kasa da mako guda kafin a fara gasar kwallon Afirka ta 'yan wasa da ke bugawa a gida da Aljeriya za ta dauki bakunci, kasar Maroko mai rike da kofin sau biyu ta yi barazanar kauracewa gasar muddin Aljeriya ba ta ba su damar jigilar 'yan wasansu ta hanyar amfani da jirgin samansu ba. Ana ganin cewa rikicin diflomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu ne, ya haddasa tsamin dangantaka har a fannin motsa jiki tsakaninsu. Da ma dai tun a shekara ta 1994 kasashen biyu suka rufe kan iyakarsu, kana babu tashin jirage kai tsaye tsakanin kasashen biyu na Magrib. Tawagogi 28 na 'yan wasan Afrika da ke taka leda a cikin gida ne, za su kece raini tsakaninsu daga ranar 13 ga wannan wata na Janairu zuwa 04 ga Fabrairu a kasar ta Aljeriya.
Kasar Guinea-Bissau, ta sauya sunan daya daga cikin filayen wasanta zuwa Pelé domin girmama sanannen gwarzon kwallon na duniya da ya rigamu gidan gaskiya a ranar 29 ga watan Disambar bara. Filin wasan dai yana Bafala ne birni na biyu mafi girma a kasar, kuma yana da kujeru dubu 15. Gwamnatin ta Guinea-Bissau ta kasance kasar Afirka ta biyu da ta sauya sunan filin kwallon kafa zuwa Pelé ba ya ga tsibirin Cape Verde da ta kasance ta farko da ta sauya sunan filin wasa na babban birnin kasar Praia, domin karrama Pelé. Su dai kasashen biyu sun amsa kiran da shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya Gianni Infantino ya yi ne, inda ya nemi kowace kasa mamba a hukumar ta FIFA ta sanya wa daya daga cikin filayen wasanninta sunan fitaccen dan kwallon na kasar Brazil. A yankin Latin Amirka kuwa, lamarin bai tsaya ga filayen wasanni ba har ma ya kai ga radawa jarirai sunan Pelé!. An kiyasta cewar fiye da jarirai 738 'yan kasar Peru da aka haifa a baya-bayannan, an sanya musu suna "Pelé" domin tunawa da dan kwallo daya tilo da ya lashe kofin duniya har sau uku karkashin tawagar Brazil.
A wasannin mako na 16 na lig din Spain La Liga da suka gudana a karshen mako, zakarar kwallon kasar wato Real Madrid ta sha kashi a filin wasa na Villeréal da ci biyu da daya. Sai dai kasancewar dukkan kwallaye biyu da aka zura wa Real Madrid bugun fenariti ne, ya sa magoya bayanta a babban birnin Spain nuna rashin jin dadinsu game da alkalancin wasan. Amma a martanin mai horas da 'yan wasan Real Carlo Ancelotti ya ce babu kuskuren alkalanci, idan aka danganta da sabbin dokoki. A Ingila kuwa, a karshen mako ne aka gudanar da wsannin kalubale na neman lashe kofin kwallon kafar na kasar. Manchester City ta lallasa FC Chelsea da ci hudu da nema a daya daga cikin wasannin da aka jira a zagaye na uku. Dan wasan kasar Aljeriya Ryad Mehrez ya yi nasarar zura kwallaye biyu da suka hada da bugun daga kai sai mai tsaron gida, lamarin da ya sa mai horas da 'yan wasa na Manchester City Pep Guardiola yaba masa.
A Faransa kuwa an sabunta kwantiragin mai horas da 'yan wasan babbar kungiyar kwallon kafa ta maza Didier Deschamps. Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Faransa Noël Le Graët ne ya tsawaita kwantiragin Didier Deschamps har zuwa 2026, shekaru 10 bayan fara wannan aiki. Wannan dai bai zo wa kowa da mamaki ba, bayan kai wa wasan karshe da Faransa ta yi a gasar cin kofin duniya a Katar. Da farko dai an tsammaci Zinedine Zidane ne zai samu damar horas da tawagar da Faransa, amma shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Faransan Noel Le Graet ya yi ikirarin cewa bai tattauna da Zinedine Zidane ba guda daga cikin masu neman mukamin horas da tawagar Faransan. Sai dai wannan furunin na Le Graet ya haifar da cece-kuce a kasar.
Dan wasan Tennis din kasar Sabiya Novak Djokovic wanda ke matsayi na biyar a duniya a yanzu a jerin gwanayen ATP, ya lashe gasarsa ta farko bana a Adelaide na kasar Ostireliya, inda ya doke dan Amirka Sebastian Korda da ci shida da bakwai da bakwai da shida da shida da hudu. Dadin dadawa ma dai, Djokovic zai halarci gasar Australian Open ta gaba da aka shirya gudanarwa daga 16 zuwa 29 ga watan Janairun da muke ciki. Wannan dai na zaman awani kokari na lashe gasar Grand Slam ta farko a kakar wasa ta bana a karo na 10, kuma ta haka ne kawai zai iya kafa tarihin lashe manyan gasanni da Rafael Nadal ya yi sau 22.